Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (2024)

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (1)

Bayani kan maƙala
  • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Abuja
  • Twitter, @abdulahidiginza
  • Aiko rahoto daga Abuja

Zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a Najeriya tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agusta ta zo ta wuce, sai dai ta bar abubuwa da dama wadanda za su zamo darasi ga al’umma.

Waɗanda suka shirya zanga-zangar, sun ce ta samu karɓuwa da nasarori a faɗin ƙasar sakamakon irin goyon bayan da suka samu a faɗin ƙasar.

A cewar Dr. Audu Bulama Bukarti, wani ƙwararren lauya kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum zanga-zangar ta yi tasiri a fanni daban-daban, domin kuwa ko ba komai ta nuna cewa yanzu mutane sun fara gajiya da irin halin matsin da suke ciki.

''Hakan ya nuna cewa tasirin zanga-zanga ba zai taɓa dusashewa a ƙasar ba, musamman yankin arewacin ƙasar,'' in ji Bukarti.

Haka shi ma Deji Adeyanju ɗaya daga cikin lauyoyin ƙungiyar 'Take it Back' ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka jagoranci zanga-zangar ya ce ‘‘zanga-zangar ta samu nasara da karɓuwa a Najeriya, duk kuwa da irin barazanar hukumomi da kame da jami'an tsaro suka riƙa yi wa masu shirya ta, don hana su gudanar da 'yancin da kundin tsarin mulki ya ba su ’’.

Sai dai zanga-zangar ta fito da abubuwa da dama, waɗanda a baya ba a yi tunanin samun su ba, kafin fara ta.

Irin wadannan abubuwa su ne:

Tarzoma da ƙone-ƙone

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (2)

A wasu wuraren zanga-zangar da tun da farko masu shirya ta suka ce ta lumane ce, ta rikiɗe zuwa tarzoma, inda aka samu arangama tsakanin jami'an tsaro da wasu masu zanga-zangar.

Irin wannan tarzoma ta haddasa ƙone-ƙone da fashe-fashen muhimman wurare, tare da sace dukiyoyin gwamnati da na jama'a.

An samu irin wannan tarzoma a Kano inda aka yi ta ƙona tayoyin tare da yunƙurin shiga gidan gwamnati da kuma lalata cibiyar koyar da fasahohi ta ƙasa da ake kira Digital Park, sannan aka fasa wani gidan ajiyar kayan abinci a kusa da gidan gwamnati inda aka sace ɗimbin kayan abincin da ke gidan.

Haka ma an samu irin wannan a jihohin Jigawa da Yobe da Kaduna da Katsina.

Lamarin da ya sa jami'an tsaro suka riƙa harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zangar a wasu wurare.

Sai dai Dr. Bukarti ya zargi jami'an tsaron da raina ajawalin mutanen yankin arewacin ƙasar, domin a cewarsa abin da suka yi a arewa suka sha, to ba za su iya yinsa a yankin kudancin ƙasar ba.

An dai samu rahoton cewa jami'an tsaro sun harbi wasu masu zanga-zangar tare da kashe su. Kodayake babban sifeton 'yansanda ƙasar ya musanta hannun 'yansanda a harbin masu zanga-zangar, to amma jami'an sojoji sun amince da kisan wani matashi a Zariya.

Sajewar ɓata-gari cikin masu zanga-zanga

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (3)

Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa ɓata-gari sun yi musu kutse cikin gangamin nasu, insa suka haddasa ɓarna mai tarin yawa a lokacin zanga-zangar.

Dr. Bukarti ya ce hakan kuwa ba ya rasa nasaba da rashin tsari da jagorancin zanga-zangar daga yankunan arewacin ƙasar.

''Idan za a shirya zanga-zanga dole ne a samu tsayayyen shugabanci, wanda zai ria bayar da umarni tare da hani a lokacin zanga-zangar, amma in ba a samu wannan ba to dole ne a samu sajewar ɓata-gari cikin zanga-zangar, waɗanda za su lalata abubuwa kamar yadda muka gani'', in ji ƙwararren lauyan.

Dama dai tun da farko masu zanga-zangar sun ce ta lumana za su shirya, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar, za su gudanar da ita bisa tsari ta tanadin doka.

To sai dai bayan fara ta da safe zuwa tsakar rana masu zanga-zangar sun zargi ɓata-garin da sacewa cikinsu domin tayar da tarzomar a wasu biranen ƙasar, irin su Kano da Jigawa da Kaduna da katsina da Yobe da Maiduguri.

To sai Dr. Bukarti ya ɗora alhakin hakan kan jami'an tsaro, waɗanda ya ce su ne suka riƙa razana masu ilimi daga cikin masu kiraye-kirayen zanga-zangar, har suka janye jikinsu, suka bar ta a hannun wadanda ba su da ilimin zanga-zangar.

'Yan siyasa a ƙasar sun yi ta zargin juna da hannu wajen ɗaukar nauyin ɓata-garin do,in shiga cikin masu zanga-zangar don tayar da tarzoma.

Fitowar almajirai zanga-zanga

A baya-bayan hukumar kula da ilimin almajari ta ƙasar ta nuna damuwarta kan yadda ta ce almajirai sun fito zanga-zangar tsadar rayuwar.

To amma a ganin Barrista Bukarti almajirai su ne mutanen da ya kamata su fito wannan zan-zangar.

''To wai a halin da ake ciki idan almajiri bai fti zanga-zangar yunwa ba, to waye ya kamata ya fito?, shi ma sai an ci an ƙoshi sannan ake ba shi ya ci, to yanzu waye yake ci ya ƙoshi har ma ya bai wa almajirin?'', in ji Bukarti.

Lauyan ya ƙara da cewa masu ci sau uku su ƙoshi a shekaru uku da suka wuce a yanzu ba lallai ya ci sau guda ya ƙoshi ba.

''To ko ka ga ai almajirai dole su shiga cikin ƙarin yunwa'', in Dr. Bukarti.

Dokar taƙaita zirga-zirga

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (4)

Bayan tarzomar da aka samu sakamakon zanga-zangar hukumomi a wasu jihohin ƙasar musamman na arewacin ƙasar sun riƙa sanya dokokin taƙaita zirga-zirga, domin daƙile yaɗuwar tarzomar da aka samu.

An sanya irin wannan doka a jihohin Borno da Yobe da Plateau da Jigawa da Kano da Kaduna da Katsina da sauransu.

Tashin farashin kayayyaki

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (5)

Sakamakon sanya dokar ta-ɓaci a wasu jihohin ƙasar, ya sa farashin kayyaki musamman na abinci sun yi tashin gwauron zaɓɓi.

Bayan sassauta dokar hana fita da ka sanya a jihar Kano, shugaban ƙungiyar masu gidajen biredi a jihar ya koka cewa farashin buhu fulawa ya yi tashin da ta tayar musu da hankali.

Inda ya yi kira ga 'yan ƙungiyarsa da su dakatar da sayen fulawar daga hannun 'yan kasuwa sakamakon tsadar da ya ce ta yi.

Haka ma batun yake ga sauran kayyakin abinci, an samu rahoton tashin farashinsu.

Tasirin shaf*ckan sada zumunta

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (6)

Asalin hoton, Getty Images

An kuma ga yadda shaf*ckan sada zumunta suka yi tasirin wajen shirya wannan zanga-zanga.

Tun da farko dai 'yan ƙasar sun fara nuna damuwarsu da koke-kokensu kan matsin rayuwa da tattalin arziki da ake a shaf*ckan sada zumunta.

Daga bisani kuma suka fara kiraye-kirayen gangamin zanga-zangar, a shaf*ckan, suka kuma sanya ranar fara ta da lokacin da za a ɗauka ana gudanar da ita, kafin a fantsama kan titunan ranar 1 ga watan na Agusta kamar dai yadda aka tsaka a shafunkan.

Hakan ya nuna cewa ta hanyar shaf*ckan sada zumunta 'yan ƙasar za su iya isar da saƙo da bayyana abinda ke damunsu har ma ya je inda ake buƙata fiye da yadda ake tsammani.

Tasirinta a arewa

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (7)

Zanga-zangar ta fi tasiri a jihohin arewacin ƙasar, saɓanin jihohin kudanci.

Dr. Bukarti ya ce hakan ya nuna cewa 'yan arewa fa sun fara yunƙuri domin bayyana abubuwan da ke damunsu.

''Yunwa da ke cinsu da rashin tsaron da ke damunsu, ya sa sun fara yunƙurin nemar wa kawunansu mafita da sauki'', in ji shi.

''Abin da hakan ke nunawa shi ne abin da da Hausawa ke cewa kan mage ya waye, mutane sun fara tunanin cewa lallai fa dole su tashi domin nemana wa kansu mafita''.

An ga yadda yadda masu zanga-zanga suka fito a kusan mafi yawan jihohin arewacin ƙasar, amma a jihohin kudanci idan ka cire Legos da Rivers babu wata jihar kudancin ƙasar da zanga-zangar ta yi tasiri.

Sai dai Dr. Bukarti ya danganta hakan kan yadda yankin arewacin ƙasar ya fi fuskantar talauci da matsin rayuwa.

''Da ma su yankin kudancin Najeriya talaucinsu ba kai na yankin arewacin ƙasar ba, su yankinsu ya fi na arewacin ƙasar wadata da ƙarfin sayen abubuwan masurufi'', in ji.

Haka kuma Barista Bukarti ya ce wani dalilin da ya sa 'yan yankin kudancin ƙasar ba su fito zanga-zangar ba shi domin suna ganin shugaban ƙasar ya fito daga yankinsu ne, don haka idn suka fito zanga-zanga tamkar sun kware masa baya ne.

Tilasta wa shugaban ƙasa yin jawabi

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (8)

Asalin hoton, Fadar Shugaban Ƙasa

Zanga-zangar ta tilasta wa shugaban ƙasar Bola Tinubu, yin wa a'ummar ƙasar jawabi a lokacin da ake tsaka da gudanar da ita.

Bayan fara ta ranar 1 ga watan Agusta, a ranar 4 ga watan ne shugaban ƙasar ya fito ya yi wa 'yan ƙasar jawabi da aka yaɗa kai-tsaye ta kafofin yaɗa labaran ƙasar.

Dr. Bukarti ya ce jawabin shugaban ƙasar alama ce da ke nuna tasirin zanga-zangar, domin kuwa a cewarsa duk abin da zai sa shugaban ƙasa ya fito ya yi bayani, to lallai ba ƙaramin abu ba ne.

A cikin jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zangar da su dakatar tare da rungumar hanyoyin sulhu, sannan ya yi wa 'yan ƙasar bitar ayyuakn ci gaba da gwamnatinsa ta bijiro da su domin amfanin 'yan ƙasar.

To sai dai masu shirya zanga-zangar sun ce jawabin shugaban ƙasar bai taɓo buƙatunsu ba, don haka ne suka ce sun yi watsi da kiran nasa na jingine zanga-zangar, inda suka sake fitowa kan tituna a ranar Litinin 5 ga watan Agusta, kwana gudan bayan jawabin shugaban ƙasar, musamman a jihar Kaduna.

Lamarin da ya sa hukumomin jihar sanya dokar taƙaita zirga-zigar a jihar, kodayake daga baya an sassautata tare da ɗage ta.

Raunin jagorancin malamai da sarakuna

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (9)

Asalin hoton, Getty Images

Zanga-zangar ta fito da raunin jagorancin sarakunan gargagiya da malaman addini, waɗanda suka yi ta kiraye-kirayen kada a gudanar da ita, amma duk da haka sai da aka bijire musu.

Dr. Bukarti ya ce ''hakan na nuna cewa a yanzu a arewa babu wanda za a yi amfani da shi wajen hana matasa nema wa kansu 'yanci''.

An ga yadda matsa suka riƙa bijire wa malaman addini da ke kiraye-kirayen kada a gudanar da ita.

Akwai wani bidiyo ma da ya ɓulla a shaf*ckan sada zumunta inda wani matashi ya yi kiran cewa duk malamin da ya hau mumbari ya ce kada a fita zanga-zanga to matasa su rikito da shi daga kan mimabrin, kodayke daga bisani matashin da ya yi bidiyon ya fito ya bayar da hakuri tare da goge shi daga shafinsa.

Tilasta wa gwamnati aiwatar da wasu tsare-tsare

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (10)

Barista Bulama Bukati ya ce zanga-zangar ta tilasta wa gwamnati da shugaban ƙasar aiwatar da wasu tsare-tsare da manufofin gwamnati da nufin daɗaɗa wa 'yan ƙasar.

''Tun kafin zanga-zangar shugaban ƙasar ya kira 'yan kwadoga domin cimma matsaya kan mafi ƙanƙantar albashi, wanna duk an yi ne domin lallaɓa masu zanga-zangar'', in ji shi.

Dr. Bukarti ya kuma barazanar zanga-zangar ce ta sa shgaban ƙasa ya amince da sayar wa matatar mai ta Dangote da ɗanyen mai da kuɗin naira.

Haka kuma ya ce zanga-zangar ta tilasta wa malaman addini da sarakuna zuwa su ga shugaban ƙasar domin ɗaukar matakan da suka dace.

''Kuma ziyarar ta su ta ƙara wa shugaban ƙaimi wajenmagance halin da ake ciki'', in ji shi.

Sannan ya ce zanga-zangar ta tilasta wa wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar fitowa kafofin yaɗa labaran ƙasar suna haƙurƙurtar da jama'a, tare da cewa za su ɗauki mataki.

Yunƙurin kafa jam'iyyar matasa

Dakta Bukarti ya ce wani babban tasiri da wannan zanga-zanga ta yi shi ne yanzu matasan ƙasar sun fara haɗa kansu tare da yunkurin kafa jam'iyyarsu ta kansu domin shiga zaben 2027.

''Kuma wannan indai da gaske suke kuma suke riƙe wanann tafiya har nan da shekara uku, yo ita mai tabbatar maka za a sha mamaki musamman a yankin arewacin Najeriya''.

Daga ƙarshe Bukarti ya ce zanga-zangar ta yi tasiri, sannan kuma idan ba a magance matsalolin yunwa da talaucin da ake ciki ba to lallai tsugune ba ta ƙare ba.

Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya - BBC News Hausa (2024)

References

Top Articles
Enzo Fernández | "Ningún país colonialista nos va a amedrentar": el gobierno de Milei defiende a los jugadores de la selección Argentina en medio del escándalo por los cánticos racistas - BBC News Mundo
Syrie Funeral Home Obituary
PBC: News & Top Stories
Evil Dead Rise Review - IGN
Buhl Park Summer Concert Series 2023 Schedule
Burkes Outlet Credit Card Sign In
East Bay Horizon
What to see and do in Spokane, Washington
What is international trade and explain its types?
The Canterville Ghost Showtimes Near Northwoods Cinema 10
Rick Harrison Daughter Ciana
Nashville Tranny
Island Cremations And Funeral Home
Lojë Shah me kompjuterin në internet. Luaj falas
Topeka Pets Craigslist
Faotp Meaning In Text
Lynchburg Arrest.org
Real Estate Transfers Erie Pa
Paperless Pay.talx/Nestle
Booty Chaser Bingo Locations In Minnesota
Rimworld Prison Break
Alvin Isd Ixl
Mo Money Login
Learning The Hard Way Chapter 4
Justified - Streams, Episodenguide und News zur Serie
Craigs List Jonesboro Ar
Costco Gas Price City Of Industry
Christmas Song Figgerits
Accuweather Mold Count
rochester, NY cars & trucks - craigslist
Devon Lannigan Obituary
Loss Payee And Lienholder Addresses And Contact Information Updated Daily Free List Bank Of America
Twitter Jeff Grubb
Funny Marco Birth Chart
Zuercher Portal Inmates Kershaw County
Societe Europeenne De Developpement Du Financement
Mo Craiglist
Pick N Pull Near Me [Locator Map + Guide + FAQ]
What Time Moon Rise Tomorrow
Sa 0 Spn 2659 Fmi 18
Bullmastiff vs English Mastiff: How Are They Different?
Melissa Black County Court Judge Group 14
Craigslist/Lakeland
Ourfig
My Compeat Workforce
Carabao Cup Wiki
Son Blackmailing Mother
Ups Carrier Locations Near Me
Sutter Health Candidate Login
Wv Anon Vault
Sir Anthony Quayle, 76; Actor Won Distinction in Theater, Film, TV
Fantasy Football News, Stats and Analysis
Latest Posts
Article information

Author: Errol Quitzon

Last Updated:

Views: 5956

Rating: 4.9 / 5 (59 voted)

Reviews: 82% of readers found this page helpful

Author information

Name: Errol Quitzon

Birthday: 1993-04-02

Address: 70604 Haley Lane, Port Weldonside, TN 99233-0942

Phone: +9665282866296

Job: Product Retail Agent

Hobby: Computer programming, Horseback riding, Hooping, Dance, Ice skating, Backpacking, Rafting

Introduction: My name is Errol Quitzon, I am a fair, cute, fancy, clean, attractive, sparkling, kind person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.